Duk da alkawalin da kasashen Turai suka dauka na ware euro biliyan 2 domin tallafawa kasashen Afrika, wajen tunkarar magance matsalar kwararar bakin haure dake shiga nahiyar turai ta Teku, bai hana wasu shuwagabanin Afrika nuna bacin ransu da matsin lambar da kasashen Turai ke yi masu ba, Shugaban kasar Senegal Macky Sall wanda ke shugabantar kungiyar kasashen yammacin Afrika CEDEAO, ya ce bakin hauren nahiyar Afrika dake zuwa Turai, basu taka kara suka karya ba, idan aka auna da wadanda ke shiga nahiyar daga yankin gabas ta tsakkiya, to kuma maye abin tada jijiyoyin wuya akan yan Afrika
Wannan matsayi na Shugaban kasar ta Senegal, ya samu goyon bayan wasu shuwagabanin Afrika, inda takwaransa na kasar Cote d’Ivoire Alassan Watara, ya ce kasarsa babbar misali ce, inda kashi 25 cikin 100 na al’ummarta ne kawai ke rayuwa a ketare.
A nasa bangaren shugaban kasar jamhuriyar Niger Mahamadu Isufu cewa ya yi, tallafin Euro Miliyan 78 na kasashen Turan suka ce, za su baiwa kasashen Afrika ba su taka kara suka karya ba, wajen tunkarar matsalar kwararar bakin hauren.
Asusun bada lamani na Duniya IMF ya ce, biliyan 1,8 na euro da aka ware domin magance matsalar kwararar bakin hare mataki mai kyau, to' amma kudi kawai, ba su isa su kawar da matsalar ba. 289